'Mutane 49 sun rasa rayukansu a Maiduguri'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani hari da Boko Haram ta kai a kan wata kasuwa a Maiduguri a baya

Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya, wato NEMA, ta ce mutane 49 ne suka rasa rayukansu a hare-haren bam din da aka kai ranar Asabar a wurare uku daban-daban a birnin Maiduguri.

Babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar arewa maso gabas, Alhaji Muhammad Kanar, ya ce wadansu mutanen 56 kuma suna asibitoci daban-daban na birnin, inda ake kula da su.

An kai hari na farko ne dai a Tashar Baga, inda wadanda suka shaida faruwar lamarin suka ce 'yan kunar-bakin-wake ne a keke mai kafa uku suka tashi bam din da suke dauke da shi.

A Kasuwar Litinin (Monday Market) kuma, wani dan kasuwa ya shaida wa BBC cewa wata 'yan kunar bakin-wake ce ta tashin bam din da ke jikinta, yayin da ake duba ta da na'urar tantance ko mutum na dauke da karfe.

Jim kadan bayan nan kuma, a cewarsa, sai 'yar kunar-bakin-wake ta biyu ta tashi bam din da take dauke da shi a wata jakar Bagco.

Wani mai rabon shan ruwa a tashar Borno Express—wuri na uku da aka kai harin—ya bayyana cewa suna tsaye suka ga wani saurayi wanda bai wuce shekara 16 ba ya wuce su dauke da wani abu a hannunsa.

Ya kara da cewa suna shirin yi masa magana sai ya danna abin bam din da ke jikinsa ya tashi.

A 'yan kwanakin nan dai hare-hare irin wadannan sun karu a wadansu sassan arewacin Najeriya, kuma hukumomi na cewa matsin lambar da sojoji ke yi a kan mayakan Boko Haram ce ta haddasa hakan.

Karin bayani