An kai hari wani gidan rawa a Mali

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keit Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mali dai ta dade ta na fuskantar hare-haren masu kaifin kishin islama da 'yan tawaye Azbinawa.

An kashe mutane hudu a wani hari da wasu masu tsattsauran ra'ayi suka kai a wani gidan rawa dake Bamako babban birnin kasar Mali.

Wani wakilin BBC a wurin ya ce ka na shiga Kulup La Terrace za ka yi karo da gawar wani bature yashe a kasa, wanda dakarun sojin Fransa da suka isa wurin jim kadan da kai harin suka ce dan kasar su ne, an kum aharbe shi har lahira da bindiga mai sarrafa kan ta.

Sauran mutanen da suka mutu sun hada da wani dan sandan kasar ta Mali, da kuma wani mai tsaron kofa na gidan rawar, shi ma dan kasar sai kuma wani bature da ake kyautata zaton dan kasar Belgium ne da aka jefawa motar da yake ciki gurneti a gefen titin da gidan rawar yake.

Wadanda suka ga abinda ya faru sun shaidawa BBC cewa sun ga wasu mutane hudu sun fita a guje a cikin wata mota, inda wani mutum guda ya dafa musu baya akan babur, sun kuma ji daya daga cikin maharan ya kabbarar ''Allahu Akbar''.

Tun da fari sakatare janal na MDD Banki Moon ya bukace gamayyar 'yan tawayen Azbinawa a Mali da su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, wadda za ta janyo kwanciyar hankula a arewacin kasar.

An dai cimma wannan yarjejeniya ne a kasar Algeria a makon da ya wuce, wadda tuni gwamnatin Mali da kungiyoyin 'yan a ware guda shida suka rattabawa hannu.

A shekarar 2012 ne masu kaifin kishin Islama na kasar Mali suka karbe iko da kusan rabin arewacin kasar. Sai dai dakarun hadin gwiwa da sojin Fransa ke jagoranta sun yi nasarar fatattakarsu a shekarar 2013.

Sai dai har yanzu akwai burbushin 'yan tawayen Azbinawa da tsirarun masu kaifin kishin Islamar na ci gaba da kaddamar da ayyukansu a cikin kasar.