Katin dindindin: INEC ta kara mako biyu

Image caption Farfesa Attahiru Jega, Shugaban Hukumar zabe ta Najeriya

Hukumar zaben Najeriya ta kara wa'adin aikin raba katin zabe na dindindin da makonni biyu, bayan cikar wa'adin bayar da katunan.

A cewarta, ta dauki matakin ne bayan fahimtar da ta yi cewa akwai mutane da dama da suka cancanci kada kuri'a amma ba su samu damar karbar katin nasu ba a tsawon wa'adin da ta kara na baya-bayan nan.

Jihar Ogun da babban birnin tarayya, Abuja sun kasance wuraren da rashin fitowar mutane su karbi katin nasu ya fi kamari.

Sai dai kuma hukumar zaben ta ce ta raba kashi 80 cikin 100 na katin, abin da da take bayyanawa da babbar nasara.

Yanzu dai kimanin makonni uku ne suka rage a fara manyan zabukan kasar.