Boko Haram: An raunata dakarun Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun kasar Chadi sun kwato wasu garuruwa daga kungiyar Boko Haram

Rahotanni daga garin Diffa a Jamhuriyar Nijar sun nuna cewa an kai wasu daga cikin dakarun kasar da aka raunata a fafatawar da suke yi da kungiyar Boko Haram a Najeriya.

Wasu mazauna birnin Diffa sun shaida wa BBC cewa, sun ga an kawo wasu dakarun Nijar wadanda aka jikkata zuwa asibiti.

A ranar Lahadi ne dakarun Nijar da na Chadi suka tsallaka zuwa Najeriya domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Mutane da dama a Diffa sun ce sun ga motocin soji kusan 200 cike da dakaru suna dannawa zuwa Najeriya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi wa shugaban kungiyar IS mubaya'a.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a Najeriya.