Sojojin Chadi da Nijar sun kwato Damasak

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Chadi sun shiga Najeriya a ranar Lahadi

Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa dakarun Chadi da na Nijar sun kwato garin Damasak daga hannun 'yan Boko Haram.

Wani mazaunin garin Damasak na jihar Borno ya shaida wa BBC cewa an kashe mayakan Boko Haram da dama a tashin hankalin.

Tun a cikin watan Nuwambar shekarar 2014 ne 'yan Boko Haram suka kwace iko da garin Damasak da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Wata majiyar tsaro a kasar Chadi ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kashe 'yan Boko Haram kusan 200 a gumurzun da aka yi a Damasak.

Majiyar ta ce kuma an hallaka dakarun Chadi 20 tare da raunata wasu 20.

A ranar Lahadi ne dakarun Nijar da na Chadi suka tsallaka zuwa Najeriya domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Mutane da dama a Diffa sun ce sun ga motocin soji kusan 200 cike da dakaru suna dannawa zuwa Najeriya.