Malami ya kashe dalibinsa a Masar

Hakkin mallakar hoto n
Image caption An haramta duka a makarantun Masar amma har yanzu malamai na yi wa yara bulala.

Ana gudanar da bincike a Masar kan mutuwar yaro dan shekara goma sha daya sakamakon dukan kawo wuka da daya daga cikin Malamansa ya yi masa.

A ranar Alhamis ne aka garzaya da yaron asibiti daga makarantarsa da ke birnin Alkahira domin duba ba shi.

Ya rasu ranar Lahadi sakamakon mummunan raunin da ya ji a kansa.

An dai dakatar da malamin da ya yi dukan daga aikinsa a wata makarantar gwamnati da ke unguwar marasa galihu, kuma 'yan sanda na gudanar da bincike a kansa.

Ana tuhumarsa da yin amfani da karfin tuwo wajen dukan yaron, wanda har hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Duk da cewa an haramta azabtarwa, amma har yanzu makarantu a Masar na yi wa yara bulala a matsayin horo.