India: An kama mutane 21 a kan fyade

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Matsalar fyade na ci gaba da ta'azzara a India

'Yan sanda a India sun kama mutane 21 da suka kashe wani mutum da ake zargi da fyade bayan sun fito da shi daga gidan yari.

Mutanen dai sun yi wa mutumin mai suna Syed Sharif Khan dan banzan duka, tare da jansa a kan titi bayan sun yi masa zigidir, sannan suka rataye shi a Dimapur, babban birnin jihar Nagaland, bayan masu zanga-zanga sun fito da shi daga gidan yari.

Daruruwan 'yan sanda ne ke kai-kawo a kan titunan Dimapur tun bayan aukuwar lamarin.

Wani babban jami'in 'yan sanda, Wabang Jamir, ya ce "A yanzu dai muna kokarin gano ko wadannan mutane na da hannu wajen kisan mutumin bayan samun su da hannu a zanga-zangar da aka yi, tare da fito da Mista Sherif daga gidan kaso".