Ni na sa Crimea ta bar Ukraine - Putin

Image caption An sha yin ce-ce-kuce akan hadewar Crimea da Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince a karon farko cewa shi ne ya bayar da umurnin kwace yankin Crimea dake Ukraine.

A cikin wani shirin talibijin da ake shirin nunawa a kasar, Mr Putin ya yi bayani a kan yadda ya umurci shugabannin jami'an tsaronsa domin su fara aikin dawo da yankin Crimea karkashin ikon Rasha, makonni kafin mayakan sa-kai su karbe ikon yankin.

'Yan kwanakin kadan da bayar da umurnin a watan Fabrairun bara, wasu sojoji suka karbe ikon Majalisar dokokin Crimea, yayin da 'yan majalisar su ka yi gaggawar kada kuri'a dominn zaben sabuwar gwamnati.

A ranar 18 ga watan Maris ne kuma Crimea ta hade da Rasha, abin da ya jawo kasashen duniya suka yi ta yin Allah-wa-dai.