Jirgin mai amfani da hasken rana ya tashi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin sama mai amfani da hasken rana ya tashi a karon farko

A ranar Litinin ne wani jirgi mai amfani da hasken rana, mallakar kasar Swiss, ya fara tashi a Abu Dhabi.

Jirgin mai daukar mutum daya kacal yana da fuka-fukai masu zuko hasken rana sannan yana da nauyi kwatankwacin nauyin mota.

Wasu matuka jirgi 'yan kasar Swiss ne su ke yin karbebeniya wajen tuka jirgin.

Jirgin zai yi shawagi ya kuma bi ta Myanmar da China da Hawaii da kuma New York kafin daga bisani ya dawo Abu Dhabi, ba tare da amfani da man jirgi ba.