Hadarin tuka tireloli zuwa yankunan Boko Haram

Yadda rikicin Boko Haram ke shafar direbobin manyan motoci.

Direbobin manyan motoci a Nigeria wadanda su ka tsallake rijiya da baya daga hare-haren Boko Haram na shan iska a karkashin wani gini.

Mafi yawa daga cikin direbobin na tuka tankokin dakon man feutur da na kananzir ne da ke jigila tsakanin Maidugiuri, birnin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka yi wa ka-ka-gida, a arewa maso gabashin kasar.

Matukan wadanda suka taru a tashar manyan motoci ta Ogbere, kimanin kilomita 50 daga arewacin Lagos, sun ce dukkaninsu rikicin na shekaru 6 da ya-ki ci ya-ki cinyewa yana shafar rayuwarsu.

Image caption Direbobin kan shafe makonni a tashar tireloli ta Ogbere kafin su samu izinin yin lodi

Atiku Abubakar na daya daga cikin direbobin, ya ce "Dukkanmu muna damuwa da yanayin, an kasha 'yan uwanmu, an sace matanmu da 'ya'yanmu an kuma kona gidajenmu."

Shi da abokansa sun bayyana irin tsananin wahalar da suke sha a jigilar da suke yi tsakanin Maiduguri zuwa Lagos.

Su kan shafe akalla kwanaki biyu da rabi a kan hanyarsu ta zuwa Lagos daga Maiduguri kafin su yi lodi, sukan kuma shafe kwanaki hudu da rabi cur idan sun yi lodin man fetur daga Lagos zuwa Maidugurin.

Sun kuma ce ko da ba bu barazanar mayakan Boko Haram, suna fuskantar matsaloli na rashin kyawun hanya.

"An kashe abokaina guda goma wadanda suka bi wannan hanyar a makonni uku da suka gabata," in ji Abubakar.

'Tsoro'

"An kashe abokaina guda goma wadanda suka bi wannan hanyar a makonni uku da suka gabata," in ji Abubakar

"Da yawa daga cikin direbobin na da kyakkawan sakamakon shaidar kamala karatu," in ji Umar Hussaini mai shekaru 18, da ke taimakawa dan'uwansa a harkar tukin.

Ya kuma gabatar da Ibrahim Abdullahi, mai shekaru 25, wani tsohon dalibin jami'a wanda ya ke karanta aikin injiniya a farkon fara rikicin.

Ya fara aiki a matsayin direban tanka tun shekaru 5 da suka gabata, saboda yadda ayyukan yi suka yi karanci ga matasa, musamman ma a yankunan da rikicin ya fi shafa.

'Rashin Tabbas'

"Gaskiya ina matukar jin tsoro, idan da akwai zabin ayyuka da na sauya wannan aikin da nake yi." In ji Abdullahi.

Image caption Ana shan bakar wahala wajen facin tayar babbar mota

Dukkan direbobin sun bayyana jin zafinsu kan dage zaben shugaban kasa da aka yi daga ranar 14 ga watan Fabrairu, sun kuma yi tir da shugaba Jonathan kan kasawarsa wajen kawo karshen rikicin.

Wasunsu ma sun alakanta shugaban kasar da cewa shi ne shugaban kungiyar Boko Haram, suna kallonsa a matsayin mai hannu kan kara girman matsalar cikin shekaru.

Wasu kuwa cewa su ka yi ya yi bakam da al'amarin ne ganin cewa matsalar a arewa maso gabashin kasar take.

"Shugaba Jonathan da 'yan Boko Haram basu da wani bambamci, saboda ya yi almundahana da kudaden da ya kamata ya gyara ma na tituna," in ji Abubakar.

Ya kara da cewa ba abinda suka sanya a gaba a rayuwa sai neman kudi ido a rufe."

Image caption Ibrahim Abdullahi, Injiniya ne amma yanzu yana aiki a matysayin direban tanka

A kowacce tafiya, akan bai wa direba alawus na naira dubu goma (10, 000), a matsayin kudin yin hidimomin rayuwarsa, amma hakan zai iya sa direban ya shafe kwana da kwanaki ya na jira a tashar tireloli ta Igbere har lokacin da za a tantanceshi a yi masa lodi.