'UCI ta kauda kai a harkar shan kwayoyi'

Hakkin mallakar hoto Getty

An zargi Hukumar dake kula da wasan tseren Kekuna ta UCI da kauda kai wajen yadda ake amfani da kwayoyi masu sanya kuzari a bangaren wasan .

Bayan wani bincike da aka dauki shekara guda ana yi, masu bincike da hukumar ta nada da kanta, sun ce a karshen shekarun 1990 da kuma farkon shekarun wannan karnin, hukumar bata dauki yunkurin da ake na hana amfani da abubuwa masu kara kuzarin da gaske ba, kuma ta yi ta nuna gazawa wajen aiwatar da dokokinta.

Rahotan ya kuma zargi hukumar ta UCI da fifita dan wasan tseren kekunan nan Lance Armstong, wanda kuma daga bisani aka dakatar da shi daga shiga wasan har tsawon rayuwarsa, saboda yin amfani da kwayoyi masu kara kuzarin.

Binciken ya kammala da cewa al'adar nan ta amfani da irin wadannan kwayoyi har yanzu na nan a fagen wasan tseren kekunan, amma ba tai muni kamar yadda take a baya ba