Hukumar SSS na binciken dan- gidan Uwais

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ayyana kungiyar IS a matsayin kungiyar ta'addanci a duniya

Hukumomi a Nigeria sun ce su na gudanar da bincike akan wasu rahotanni da ke zargin cewar dan wani tsohon babban Jami'i a Nigeria ya shiga kungiyar nan ta masu da'awar Jihad ta IS da ke Syria.

Ofishin Jakadancin kasar Turkiyya ya tabbatar da cewar ya bayar da visa ga Ibrahim Lawal Uwais, wanda da ne ga tsohon babban Jojin kotun kolin Nigeria a kwanakin baya.

Ana dai jin Ibrahim Uwais ya shiga kasar ta Syria ne daga Turkiyya.

Iyalan tsohon babban jojin sun ce sun sami wannan labari ne kamar yadda sauran 'yan Nigeria suka samu, kuma tuni su ka ce sun shaidawa hukumomi a Nigeria.

Sai dai sun bayyana mamakin cewa dan su na da wata alaka da wata kungiyar ta'addanci ganin yadda yake fitowa karara ya soki kungiyar Boko Haram ta Nigeria.

An dai bayar da rahotan cewa Ibrahim ya bar Nigeria ne tare da matansa biyu da kuma yaransa hudu inda ya ce zai je yankin gabas ta tsakiya.

Mai magana da yawun hukumar SSS a Nigeria ta tabbatarwa da BBC cewa hukumar su na da labari akan Ibrahim Uwais kuma su na gudanar da bincike.