'Yan wasan Faransa sun mutu a Argentina

Image caption 'Yan wasan da suka mutu

Ofishin shugaban kasar Faransa ya ce 'yan kasar takwas ne suka mutu cikinsu har da mutane biyu da suka lashe kyautar zinare a gasar wasannin Olympics.

Mutanen sun mutu ne a lokacin da wasu jiragen helikofta biyu suka yi karo da juna a kasar Argentina.

Fasinjojin jirgin na daukar fim ne na wani shirin gidan talabijin a lokacin.

Wadanda suka mutun sun hada da Camil Muffat, 'yar wasan iyo, wanda ya lashe lambar yabo a London a shekarar 2012, da Alexis Vastine -- wadda shi kuma dan wasan damben gasar Olympics ne.

Su ma matukan jiragen biyu sun mutu a lokacin hatsarin.

Wakilin BBC ya ce shirin da suke dauka wanda ake kira 'Dropped' ya kunshi lulawa sama da irin wadannan shahararrun 'yan wasa zuwa wurare masu nisa a kasashe daban daban, da kuma daukar su fim a lokacin da suke kokarin nemo abinci da kuma makwanci.