Matsi ne ya tilasta wa Boko Haram mubaya'a ga IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau na son kafa daular Musulunci

Mubaya'ar kungiyar Boko Haram ga kungiyar IS, wata alama ce ta rauni da kuma matsin lamba da Boko Haram ke fuskantan daga dakarun Nigeria da kuma kawayenta, in ji gwamnatin Nigeria.

Mai magana da yawun gwamnati kan ayyukan ta'addanci, Mike Omeri wanda ya bayyana hakan, ya ce kungiyar na cikin tsaka mai wuya saboda yadda ake kashe mayakanta.

A karshen mako ne Abubakar Shekau wanda shi ne shugaban Boko Haram ya yi mubaya'a ga kungiyar IS a wani sako na muryarsa da aka saka a shafin Twitter.

Tun bayan da aka kafa rundunar soji daga kasashen Nigeria da Kamaru da Chadi da kuma Nijar a watan da ya gabata, alamu suka nuna galaba a kan Boko Haram inda aka kwato wasu yankunan da kungiyar ta kwace a bara.

Omeri ya ce rundunar hadin gwiwar za ta ci gaba da aikin lalata sansanonin mayakan Boko Haram tare da murkushe su.