'Yan sanda sun tarwatsa dalibai a Myanmar

Image caption Daliban na adawa ne da sabuwar dokar karatu da suka ce zata takurawa 'yancinsu.

'Yan sanda a kasar Myanmar sun yi amfani da kulake wajen tarwatsa daliban da ke zanga-zangar adawa da wata sabuwar dokar karatu da suka ce za ta takurawa 'yancinsu.

Ganau sun ce an kama dalibai da dama bayan an gaza cimma matsaya kan yadda za a sassauta dokar, lamarin da ya sa masu zanga-zangar suka yi kokarin karya shingayen da 'yan sanda suka sanya.

Kimanin dalibai 150 aka ritsa a tsakiyar birnin Letpadan tun a makon jiya a lokacin da 'yan sanda suka dakatar da jerin gwanon da suka fara.

Sun fara jerin gwanon ne daga garin Mandalay kusan wata guda da ya gabata domin nuna adawa da sabuwar dokar.