Bam ya hallaka mutane biyar a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaron da harin karshen mako ya rutsa da shi kenan

Mutane akalla biyar ne suka rasu sakamakon tashin bam da wata 'yar kunar-bakin-wake ta yi a kasuwar Monday ta Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe hudu, ya haddasa jikkatar wasu mutane kusan biyar.

Wani jami'in kula da kasuwar ya shaida wa BBC cewar sun kai gawawwakin zuwa asibiti.

Mutumin ya ce wata mata mai girman jiki ce ta tayar da bam din lokacin da mutane suke hada-hada.

A karshen mako ma mutane akalla 50 ne suka rasu sakamakon tashin bam a wannan kasuwar, lamarin da ake zargin 'yan Boko Haram da aikatawa.

A wani labarin kuma, mayakan Boko Haram sun kai hari a kauyen Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga ta jihar Borno inda suka hallaka mutane da dama.

Rikicin Boko Haram ya janyo salwantar rayukar mutane fiye da 13,000 cikin shekaru shida a Nigeria.