Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram a Gombi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sojojin sun kwato garuruwa da dama daga hannun 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta yi ikirarin hallaka mayakan Boko Haram da dama tare da kwace makamansu a yunkurin 'yan kungiyar na kai hari a garin Gombi na jihar Adamawa.

Kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka yi kokarin kaddamar da hare-hare a garin Gombe a ranar Litinin da yamma.

A cewar Kanar Kukasheka sun kwace manyan motocin Boko Haram (Hilux) hudu da manyan makamai da kuma alburusai.

Sai dai a lokacin gumurzun an hallaka sojin Nigeria daya.

Hakan na zuwa ne bayan da dakarun Chadi da na Nijar suka kwato garin Damasak na jihar Borno daga wajen 'yan Boko Haram.