Aiwatar da hukuncin kisa a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin mutane 8, 000 ne aka yanke wa hukuncin kisa a Pakistan.

Gwamnatin Pakistan ta janye dakatarwar da tayi na aiwatar da dokar hukuncin kisa a kan masu aikata manyan laifuka.

An dakatar da dokar ne kan masu aikata laifukan ta'addanci na dan lokaci, sakamakon kisan kiyashin da aka yi wa kimanin mutane 150 a wata makaranta wadanda yawancinsu yara ne a watan Disambar da ya gabata.

A yanzu dai jami'an gwamnati sun tabbatar da cewa za a koma aiwatar da hukuncin kisa a kan 'yan zaman kason da aka yanke wa hukunci wadanda suka kure dukkan matakan daukaka kara.

Da kuma wadanda aka yi watsi da neman afuwar da suka nemi a yi musu, lamarin da ya kawo karshen dakatar da aiwatar da hukunin kisa kan masu laifi na tsawon shekara 7.

Kungiyar kare hakkin dan adam, Justice Project Pakistan, ta bayyana lamarin da cewa hakan bai dace ba.

Masu fafutika sun ce fiye da mutane 8, 000 ne aka yanke wa hukuncin kisa a Pakistan.