Simone Gbagbo za ta yi zaman kaso na shekara 20

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Simone Gbagbo, matar tsohon shugaban kasar Ivory Coast

Wata kotu a Ivory Coast ta yanke wa matar tsohon shugaban kasar, Simone Gbagbo hukuncin shekaru 20 a gidan kaso saboda irin rawar da ta taka a rikicin bayan zaben shugaban kasar, a shekarar 2010.

A shekarar 2011 ne dai aka kama Simone Gbagbo tare da mijinta, Laurent Gbagbo bisa dalilan yin zagon kasa ga yanayin tsaro da kuma karfafa wa 'yan bangar siyasa gwiwa a lokacin rikicin zaben.

Shi dai mista Gbagbo yaki amince wa da kayen da yasha daga abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara wanda duniya ta bayyana da ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasar na 2010.

An ce kimanin mutane dubu uku ne suka rasa rayukansu a lokacin rikicin.

A yanzu haka, Laurent Gbagbo yana fuskantar tuhuma daga kotun hakunta manyan laifuka ta duniya da ke kasar Hague, wato ICC bisa dalilan keta haddin bil'adama.