Ukraine: 'Yan aware sun janye makamai daga bakin daga

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kimanin mutane dubu shida ne suka mutu tun bayan barkewar rikicin gabashin Ukraine a watan Aprilun bara.

Shugaban Ukraine Petro Poreshenko ya ce 'yan aware da Rasha ke goyon baya a gabashin kasar sun janye akasarinsu manyan makamansu daga bakin daga.

Da yake Magana a gidan talbijin na kasar, Mr Poroshenko ya kuma ce dakarun gwamnatinsa ma sun janye mafi yawan manyan makamansu na rokoki da atilari daga bakin dagar.

A karkashin wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanyawa hannu a watan Fabrairu, a farkon watan Maris ne ake sa ran dukkan bangarorin su janye manyan makaman nasu.

Yarjejeniyar dai tana aiki duk kuwa da yadda ake cigaba da rikicin.

Bangarorin dai na zargin juna da karya sharadin yarjejeniyar don son rai.