An ceto yara 80 daga Boko Haram a Kamaru

Hakkin mallakar hoto .
Image caption An ceto yara 80 daga sansanin Boko Haram a Kamaru

Sojojin Kamaru sun ceto yara kimanin 80 daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram a arewacin kasar.

Sojojin na musamman masu yaki da ta'addanci sun ce sun ceto yaran ne a lokacin wani samame da suka kai kan wata makarantar horas da yara akidun Boko Haram.

An kai samamen ne dai makwannin da suka gabata, bayan samun bayanai daga mutanen kauyen da sansanin yake mai kama da makarantar allo.

Yanzu haka yaran da aka kubutar su 80 suna gidajen marayu a arewacin kasar sakamakon kasa tantance mahaifansu.

An ce yaran masu shekaru 5 zuwa 18, ba sa iya fahimtar yaransu na haihuwa ballantana turanci ko faransanci.

Yayin farmakin an kama mutane 104 wadanda ake zargin sune masu shayar da yaran akidun na Boko Haram.