Ana fataucin jarirai a China

Wani binciken da BBC ta gudanar ya gano cewa ana tallata jarirai domin sayarwa a shafIkan Internet a China.. inda ake saye harkar da sunan neman masu daukarsu

BBC ta gano wani Tallan jaririya 'yar watanni 8 akan kudi dala 30,000 a shafin na Intanet.

Wakilin BBC ya ce an nuna musu hoton jaririyar a bidiyo bayan sun saje a matsayin masu saya, a lokacin da aka kira wata mata wacce tace ba za ta iya kula da jaririyar ba.

Kodayake tallan yara kanana saboda a samu wanda zai dauke su ya halartta a China, sai dai ya haramta a sanya su a kasuwa a matsayin na sayarwa

An yi kiyasin cewa yara kusan 20,000 ne ake sacewa a kowacce shekara a China, kuma an yi imanin cewa da dama daga cikinsu ana sayar da su ne.