IS na amfani da yara wajen harbe mutane

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen Muhammad Musallam kenan da kungiyar IS ta kashe rike da hotonsa.

Mayakan kungiyar IS sun fitar da wani faifan bidiyo wanda ga alamu ke nuna wani dan karamin yaro yana kashe wani fursuna balarabe dan- Israila.

A hoton bidiyon, an ga wani mutum da ya ce shi ne Mohammed Sa'id Ismail Musallam, mai shekaru 19, ya durkusa a kan kafar dan yaron, wanda shi kuma ga alamu shekarunsa ba su wuce 12 ba.

Mutumin, wanda ke magana ana nadarta a kamara, ya ce hukumar leken asirin kasar Isra'ila ce ta dauke shi aiki domin ya shiga cikin kungiyar IS a Syria sannan ya yi wa Israi'lan leken asiri.

Bidiyon, wanda ba za a iya tantance sahihancinsa ba, ya kare ne da nuna yadda dan yaron ya harbi mutumin a kansa ta hanyar amfani da wata 'yar karamar bindiga

"Wani abu mai razanarwa game da wannan bidiyon shi ne yadda aka ga yaro karami sanye da kakin soji, yana harbin Mohammed a kansa, sannan kuma yai ta harbinsa da 'yar karamar bindiga a jikinsa", in ji Wakilin BBC.