Morocco ta janye jakadanta a Nigeria

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Shugaba Jonathan na cigaba da yakin neman zabe don neman tazarce

Morocco ta janye jakadanta daga Nigeria, bayan da hukumomin kasar suka zargi Sarki Mohammed na VI da kokarin saka shi cikin yakin neman zabe.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Morocco ta musanta cewa Sarkin ya tattauna da Shugaba Goodluck Jonathan ta wayar tarho, kamar yadda aka yayata a Nigeria.

Sai dai Nigeria ta musanta zargin cewa tanason amfani da Sarkin wajen neman kuri'un Musulmi a kasar.

Mr Jonathan wanda Kirista ne daga kudancin kasar zai fafata da Muhammadu Buhari, Musulmi daga arewacin kasar a zaben shudaban kasa a ranar 28 ga watan Maris.

Ma'aikatar harkokin wajen Nigeria a karshen mako ta musanta zargin cewa Mr Jonathan ya tattauna da Sarki Mohammed ta wayar tarho, amma kuma sarkin sai ya gwale Mr Jonathan.