Nigeria: Kawunan 'yan Majalisar Dattawa sun rabu

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption An sami banbancin ra'ayi a majalisar dattawa kan tantance Sanata Obanikoro a matsayin mukamin minista

A Najeriya, an samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan majalisar dattawan kasar a kan tantance Sanata Musuliu Obanikoro, mutumin da shugaban kasar ke son nadawa a matsayin minista, lamarin da ya kai ga 'yan majalisar dattawa daga bangaren babbar jam'iyyar adawa ta APC ficewa daga zauren majalisar a ranar Laraba.

Su dai 'yan majalisar dattawan na bangaren jam'iyar adawa ta APC sun ki amincewa da Sanata Musiliu Obanikor ne bisa zargin da suke yi masa da hannu a magudin zabe.

Amma duk da haka shugaban majalisar, David Mark, da 'yan majalisar na jam'iyyar PDP mai mulkin kasar sun amice a nada shi, koda yake sun yi hakan ne bayan 'yan adawa sun fice daga zauren majalisar.

'Yan jam'iyyar APC a majalisar sun yi barazanar daukar kwararan matakai a kan shugaban Majalisar wanda suke zargi da rashin mutunta su.

Shi dai shugaban Najeriyar Goodluck ne ya gabatarwa da 'yan majalisar sunayen wasu mutane takwas ne domin su tantance su, kafin a nada su a matsayin ministoci cikinsu har da Musiliu Obanikoro.