Gwamnonin PDP sun ce ba za su sauya sheka ba

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Ana zargin wasu gwamnonin PDP za su sauya sheka

A Najeriya, wasu gwamnonin PDP sun musanta wasu rahotanni da ke cewa wasu daga cikinsu na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a wani taro da suka gudanar ranar Talata a Lagos.

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya shaidawa BBC cewa "kazamin PDP ne suka koma APC kuma ba su da ainihin abin da zai basu riba su ce za a koma wajen su".

Wani batu da ya kankane taron gwamnonin a Legas kuma shi ne batun amfani da katin dindindin na zabe, da kuma na'urar da za ta tantance masu jefa kuri'a a zaben shekara ta 2015.

Gwamnonin sun ce ba sa adawa da yin amfani da katin na dindindin, sai dai sun ce har yanzu akwai dumbun 'yan kasar da ba su karbi katunansu ba.

A ranar 28 ga watan Maris ne dai za'a gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria.