Mutane 41 sun mutu a hadarin mota a Tanzania

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Hadarin mota da aka yi a Moscow

Mutum 41 suka mutu a wani hadarin mota a kasar Tanzania, inda wata motar safa ta kara da wasu wasu motocin kaya biyu, yayin da mutum 23 suka jikkata.

'Yan sanda sun ce hadarin ya auku ne a yankin Iringa, lokacin da direban daya daga cikin motocin kayan ya yi kokarin kauce wa wani rami.

A wannan lokacin ne sai wata kwantena ta rikito daga babbar motar ta fada kan karamar motar fasinjinjo.

An saba fuskantar hadarin mota a kasar Tanzania saboda rashin kyawun hanyoyi.

'Yan sandan sun kuma ce sun kammala zakulo gawawwakin da suka makale a tsakanin manyan motocin biyu.

Ita dai motar safa din na kan hanyar ta ta zuwa Dar es Salaam babban birnin kasar ta Tanzania daga garin Mbeya lokacin da hadarin ya afku.