An kama wani mutum a kan taimakawa mata shiga IS

Hakkin mallakar hoto MET POLICE
Image caption Shamima da Amira da Kadiza dalibai ne a makarantar Bethnal Green Academy, da ke gabashin London.

Ministan harkokin wajen Turkiya, Mevlut Cavusoglu, ya ce an kama wani mutum bisa zarginsa da taimakawa wasu 'yan mata guda uku 'yan makaranta da tsallakawa zuwa Syria.

An gano cewa mutumin yana aiki ne da hukumar leken asirin wata kasa da ke cikin kungiyar kawancen mayakan IS.

An yi amanna cewa 'yan matan, Shamima Begum da Amira Abase masu shekaru 15 da kuma Kadiza Sultana mai shekara 16 sun bar Biritaniya a watan jiya domin bin sahun masu da'awar jihadin.

Har yanzu ba a gano daga wacce kasa mutumin da ya taimaka mu su din ya fito ba.

Mr Cavusoglu, wanda ya ce ya sanar wa sakataren harkokin wajen Biritaniya Philip Hammond al'amarin, ya kara da cewa "Mutumin ba dan kasar Amurka ko daya daga cikin kasashen nahiyar Turai ba ne."