Majalisar Dinkin Duniya ta gaza a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijra sakamakon tashin hankali a Syria

Wani rahoto da kungiyoyin agaji da na kare hakkin bil Adama suka fitar ya zargi kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da gazawa wajen kare 'yancin wadanda yakin da ake yi a kasar Syria ya rutsa da su.

Rahoton dai ya bayyana shekarar 2014 a matsayin wacce ta fi kowacce muni tun fara yakin kasar a watan Maris na 2011.

Alkaluman da rahoton ya fitar sun nuna cewa an kashe mutane akalla dubu 76 a shekarar 2014.

Kimanin mutane miliyan hudu da dubu dari 8 ne suke wurare da cetonsu da kai musu agaji za su yi wuya.

Har wa yau rahoton ya ce kananan yara miliyan 5 da dubu dari 6 ne suke bukatar agajin gaggawa a halin yanzu.