An mayar wa Tambuwal jami'an tsaronsa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Aminu Tambuwal ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC

Hukumar 'yan sandan farin-kaya ta Najeriya, DSS ta mayar wa kakakin majalisar wakilan kasar, Aminu Tambuwal, jami'an tsaronsa da ta janye bayan ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a shekarar 2014.

Mai magana da yawun kakakin majalisar, Malam Imam Imam, ya shaida wa BBC cewa an mayar da jami'an tsaron farin-kayan ne ranar Laraba da yamma.

Ya kara da cewa kamar yadda ba a bayar da dalilin janye su ba, haka ma ba a fada musu dalilin dawo da su ba.

Sai dai Malam Imam ya ce har yanzu ba a dawo da jami'an rundunar 'yan sanda ba, wadanda su ma aka janye a lokacin.

A watan Oktoba ne dai rundunar 'yan sandan kasar da takwararta ta 'yan sandan farin-kaya suka janye jami'ansu da ke bai wa kakakin majalisar wakilan kariya.

A wancan lokacin, 'yan sandan sun yi yunkurin hana shi shiga majalisar, suna masu cewa ya rasa matsayinsa na kasancewa shugabanta tunda ya fice daga jam'iyya mai mulki.

Sai dai Alhaji Aminu Tambuwal da wasu 'yan majalisar wakilan sun kutsa kai majalisar, kuma daga bisani ya kai rundunar 'yan sandan kara a gaban kotu.

Lamarin dai ya janyo cece-kuce a kasar, inda wasu ke ganin fadar shugaban kasar na da hannu wajen yunkurin hana shi shiga majalisar, koda yake an musanta wannan zargi.