Kotun Jamus ta amince wa mata saka kallabi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A shekara ta 2003 ne gwamnatin Jamus ta haramta wa Malamai Musulmai rufe kansu a makarantu

Babbar kotun kasar Jamus ta dage wata doka da ta sanya kan hana Malamai Musulmai rufe kansu.

Kotun ta ce tsohuwar dokar wacce aka samar a shekara ta 2003, ta keta hakkin 'yancin addini.

Wata Malama Musulma ce ta kai karar bayan da ta kasa samun wani aiki da ta nema.

Kotun ta ce za a soke bin tsari addini ne kawai idan an ga zai tabarbarewar al'amura.

An yi amanna cewa dokar za ta yi aiki ne a dukkan jihohin Jamus wadanda suka sanya dokar hana rufe kai a makarantu.

Wani kakakin jam'iyyar adawa ta Green Party ya ce wannan rana ce ta samun 'yancin addini yana mai cewa "rufe kai ba shi da wata barazana ga al'ummar Jamus kamar abokan adawa na bambanci."