Ghali Na'abba ya fita daga PDP

Hakkin mallakar hoto nass
Image caption Ghali Na'abba ya ce ba a taba samun shugaban da ya yi amfani da addini da kabilanci wajen raba kawunan 'yan Najeriyar kamar Jonathan ba.

Tsohon kakakin majalisar wakilan Nigeria, Ghali Umar Na'abba, ya ce ya fita jam'iyyar PDP saboda rashin iya shugabancin Goodluck Jonathan.

A wata wasika da ya aikewa shugabannin jam'iyyar, tsohon kakakin majalisar wakilan ya kara da cewa ya bar jam'iyyar ta PDP ne saboda rashin adalci da kuma kaucewa manufofin da aka kafa jam'iyyar a kai tun farkon ta.

A cewarsa, "Babu wata gwamnatin kasar nan da ta yi amfani da addini da kabilanci wajen raba kawunan 'yan kasa kamar gwamnatin Dr Goodluck Jonathan".

Ya ce akwai wasu manyan jam'iyyar da su ma za su fice daga jam'iyyar a kowane lokaci daga yanzu.

Gali Na'abba ya ce duk da cewa bai koma wata jam'iyya ba, amma ya ce a zabi Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a takarar shugabancin kasar a zaben wannan watan.