Banki zai yi amfani da bugun zuciya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bankin na Halifax ya ce matakin zai inganta harkar banki

Wani banki a Biritaniya zai fara amfani da wata na'ura da ke tantance bugun zuciyar masu mu'amala da shi domin rika ba su damar yin amfani da asusunsu ba tare da sun sa kalmomin sirrinsu ba.

Bankin Halifax ya ce bugun zuciyar kowanne mutum na da bambanci domin haka zai ba masu hulda da shi wani warwaro da zai rika gane bugun ziyarsu.

A cewar sa, za a hada warwaron da kwamfutar mutum domin ba shi damar shiga asusun ajiyarsa ta hanyar intanet.

Bankin na Halifax ya kara da cewa da wuya a kwaikwayi bugun zuciyar mutum, yana mai cewa amfani da bugun zuciya a harkokin banki ya fi inganci a kan daukar hoton yatsun mutum.