Putin ya 'bata', ya dawo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Putin ya bayyana a fili a karon farko tun ranar biyar ga watan Maris

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, wanda rabon sa da ya fito fili tun ranar biyar ga watan Maris, ya fito bayyana a ranar Litinin.

An gan shi ne a tare da Shugaban kasar Kyrgyzstan, Almazbek Atambayev, a garin St. Petersburg.

A makon jiya ne shugaba Putin ya soke harkoki da yawa da aka tsara zai yi.

Shugaban dai ba ya jituwa da kasashen yammacin duniya bisa katsalandan da yake yi a harkokin gidan Ukraine.