Iraki: An rusa kabarin Saddam Hussein

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu mabiya Sunna sun ce sun cire gawar Saddam daga kabarinsa

Dakarun Iraki da 'yan kato-da-gora da ke fafata wa da 'yan kungiyar IS a kusa da Tikrit sun ce an kusa lalata dukkanin kushewar tsohon shugaban kasar, marigayi Saddam Hussein.

Wani hoton bidiyo da kamfanin dillancin labaran Associated Press ya fitar ya nuna yadda aka yi kaca-kaca da yankin da kabarin yake a kauyen al-Awja.

Hoton bidiyon ya nuna yadda aka tumbuke katon hoton Saddam da aka kafa a kauyen, kana aka maye gurbinsa da tutoci da hotunan shugabannin 'yan Shia, cikinsu har da hoton wani Janar na sojinsu, Qassem Soleimani, wanda ke bayar da shawara ga 'yan Shia domin yaki da IS.

Wakilin BBC a yankin ya ce mabiyan Sunna suna zargin 'yan Shia da rusa kabarin Saddam Hussein da gangan.

A shekarar da ta gabata ne wasu mabiya Sunna suka ce sun cire gawar Saddam daga kushewarsa, sannan suka sake binne ta a wani waje da ba su bayyana ba.