An yi wa wani dashen mazakuta a Afrika ta Kudu

Image caption Wadanda aka yi wa kaciyar gargajiya a Afrika ta Kudu

Wasu likitocin da suka kware a harkar tiyata a kasar Afirka ta Kudu sun yi nasarar yi wa wani mutum dashen mazakuta.

An dai shafe sa'o'i tara ana aikin tiyatar, wanda aka yi a asibiti Tygerberg da ke Cape Town, tare da hadin-gwiwa da jami'ar Stellenbosch.

An ce wannan ne karo na biyu da aka yi irin wannan tiyata ta dashen gaba.

Likitocin dai sun ce wanda aka yi wa tiyatar ya murmure sosai.

An yi wa mutumin wannan aikin dashen al'aurar ne sakamakon larurar da ya yi fama da ita tun lokacin da aka yi masa kaciyar gargajiya, wadda ta baci har ta kai ga yanke masa gaba.