Dakarun sojin Iraqi sun nausa Tikrit

Sojojin Iraq a Tikrit Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu tada kayar baya na kungiyar IS sun mamaye wasu daga cikin biranen Iraqi.

Wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin Iraqi ke kokarin karbe iko da birnin ba, kwanaki goma kenan da dakarun sojin kasar suka ja daga ta ba gudu ba ja da baya har sai sun karbe birnin.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin Iraqi dubu uku da mayakan sa kai na darikar Shi'a kusan dubu ashirin, da wasu daga cikin mabiya darikar Sunni sun yi nasarar shiga arewacin garin Qadisiyya da ke makoftaka da Tikrit.

Wani sojan Iraqi da bai so a bayyana sunan sa ba, yace da sanyin safiyar nan dakarun sun tunkari Tikrit ta fuska hudu, ya yin da wani babban jami'in 'yan sanda ya shaidawa gidan talabijin din kasar cewa mayakan da ke marawa kungiyar masu fafutukar kafa daular musulunci baya, sun fara kwacewa mutane motoci inda suke kokarin tserewa daga birnin.

Da yake jawabi a biriin Washington hafsan hafsoshin mayakan Amurka General Martin Dempsey yace ya na da tabbacin cewa wannan karon za su yi nasara akan mayakan IS, duk da cewar ba a yi amfani da mayakan sama wajen kaiwa kungiyar hare-hare ba.

Sai dai ya yin da mayakan sa kai na darikar Shi'a da kasar Iran ke marawa baya suka kasance a sahun gaba wajen jagorantar wannan yaki, Mr Dempsey ya nuna damuwa game da makomar mabiya darikar Sunni a kasar bayan an gama yakin.