Murar tsuntsaye a Amurka

Murar tsuntsaye a Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Murar tsuntsaye a Amurka

Kasar Mexico, wadda ta zarce kowacce kasa sayen Kaji daga Amurka ta haramta higar da kaajin a yanzu daga Arkansas bayan hukumomi a can sun tabbatar da samun wasu kaji dake dauke da cutar murar tsuntsaye.

Kungiyar Tarayyar Turai da sauran wasu kasashe sun bi sahu wajen haramta shigar da kajin daga Amurka.

Gwamnatin Amurkar dai ta fada a ranar laraba cewar an tabbatar da murar tsuntsaye ga wasu talo-talo a jihar ta Arkansas wadda ita ce jiha mafi girma da ake kiwon tsantsayen.

Gwamnatin Amurkar ta ce nau'in kwayar cutar H5N2 ba shi haifar da wata barazana ga bil-adama.

Karin bayani