Volcanon Tonga ya kafa sabon tsibiri

Sabon tsibiri daga amon wuta na dutsi Hakkin mallakar hoto GP Orbassano
Image caption Sabon tsibiri daga amon wuta na dutsi

An kafa wani sabon tsibiri a tekun Pacific ta kudu bayan wani dutse dake cikin ruwa ya yi amon wuta a Tonga.

Hotunan tsibirin sun bulla a cikin ruwan a wani yanki mai nisan kilomita 45 a arewa maso yammacin Nuku'alofa babban birnin Tonga.

Tsibirin wanda yake da tsawon mita 500 an kafa shi ne bayan da dutsen dake yankin Hunga Tonga ya yi amon wuta, wadda ta fara a cikin watan Disamba.

Wani masanin kimiyya ya ce da wuya idan tsibirin zai zamo da mazauni don haka zai zamo mai hadari ga masu ziyarar sa.

Dutsen mai amon wuta - wanda cikakken sunan sa shine Hunga Tonga-Hunga Ha'apai - ya yi amon wuta karo na biyu kenan cikin shekaru biyar a cikin watan Disamba.

Hotunan Video da aka dauka daga cikin wani kwale-kwale daruruwan mitoci daga yankin da dutsen yake, sun nuna dutsen yana amon wani irin dumbujen gas wanda ke ketowa daga cikin teku.

Hotunan da aka dauka ta tauraron dan adam cikin kwanakin da dutsen ya shafe yana amon wuta, sun nuna yadda wani sabon dutse ya kafu, da kuma karin wata diddigar amon dutsen a cikin teku.

A kusa da daya daga cikin tsibirran biyu wadanda a can baya, su ne suka hada Hunga Tonga-Hunga Ha'apai akwai wani wawaken rami.

Wani Mazaunin babban tsibirin Tonga ya dauki hotunan sabon tsibirin daga saman sa.

Giapiero Orbassana wanda ya mallaki wani Otel a Tonga, ya kai ziyara tsibirin tare da wasu abokai biyu, ya kuma ce yana sa ran zai kara kai wata ziyara a wurin.

Yace, "da za ran ka hau a kansa za ka taras cewar yana da karfi, kuma yana da tsawo kwarai da gaske."

Karin bayani