An lalata komai a Gamborou - 'Yan gudun hijira

'Yan gudun hijira na Gamboru Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan gudun hijira na Gamboru

Rahotannin daga iyakar Najeriya da Kamaru sun ce wasu 'yan gudun hijirar dake gudu daga garin Gamboru na Najeriya zuwa garin Fotokol na Kamaru sun samu damar shiga garin na su a karon farko tun bayan da mayakan Boko Haram suka kama shi a bara.

Sojojin Najeriya ne dai aka ce suka baiwa 'yan gudun hijirar damar shiga garin domin ko ya'allah za su ga wani abu mai amfani da suke son koma wa da shi sansanin da suke gudun hijirar.

Wasu mutanen da BBC ta zanta da su, sun ce an lalata komai a garin, yawan gawarwakin mutane kuwa, ba su misaltuwa.

Kasuwar garin kan ta, wadda suka ce ita ce ta biyu bayan ta Maiduguri, an kone ta babu abinda ya rage a cikin ta.

Karin bayani