Mataimakin shugaban Saliyo ya nemi mafaka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dangantaka ta dade da yin tsami tsakaninsa da shugaban kasar

Mataimakin shugaban kasar Saliyo, Samuel Sam-Sumana, ya ce yana neman mafakar siyasa a ofishin jakadancin Amurka da ke babban birnin kasar, Freetown.

Tun da farko sojoji sun yiwa gidansa kawanya kana kuma suka kwace makaman dogaran da ke tsaron lafiyarsa.

Sai dai ba a bayyana wanda ya bada umarnin a yi wa gidan maitaimakin shugaban kasar kawanya ba.

A makon da ya gabata ne jam'iyyar All Peoples Congress, APC wadda ke mulkin kasar ta kori Mr. Sam-Sumana bisa zarginsa da haddasa tarzoma da coge a takardunsa na makaranta da kuma yin karya game da addininsa.

Ya dai musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, sannan ya yi watsi da kiraye-kirayen ya ajiye mukaminsa.

Kundin tsarin mulkin Saliyo bai amince a kori mataimakin shugaban kasar ba.

A watan da ya wuce Mr. Sam-Sumana ya killace kansa bayan rasuwar daya daga cikin dogaransa sakamakon cutar Ebola, domin zama babban abin koyi.