Bayan kisan mutane 81, kura ta lafa a Benue

Babban sufeton 'yan sandan Nigeria Sulaiman Abba. Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Kawo yanzu kura ta lafa a jihar ta Benue.

Rahotanni daga jihar Benue a Najeriya sun ce adadin mutane da wasu 'yan-bindiga suka kashe a yankin Agatu ya karu sosai.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin ya ce an kashe mutane tamanin da daya, yayin da wasu da dama suka jikkata, baya ga kona gidaje.

Kawo yanzu dai kura ta lafa, an kuma tura karin jami'an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Amma tuni maharan suka sulale bayan da suka kaddamar da harin da asubahin ranar Lahadi a wani kauye da ake kira Egba.

Sai dai 'yan sanda a jihar sun ce suna kyautata zaton fulani makiyaya ne suka kawo harin, ganin yadda a baya aka sha fuskantar rikice tsakanin su da manoma.

Sai dai dan majalisar da ke wakiltar yankin ya musanta zargin, yana mai cewa maharan sun kai harin ne sanye da kakin soja suka zo, kuma sun yi kitso a kawunansu.

Ya kara da cewa ba su yi kama da 'yan Nigeria ba.