'Yan bindiga sun kashe mutane 80 a Benue

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga jihar Benue a Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kashe kimanin mutane 81 a karamar hukumar Agatu.

Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar yankin, Mista Audu Sule, ya sheda wa BBC cewa an kashe akalla mutane 81, yayin da wasu da dama suka jikkita a harin.

Kawo yanzu dai kura ta lafa, an kuma tura karin jami'an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Amma maharan sun sulale bayan da suka kaddamar da harin da asubahin ranar Lahadi a kauyen da ake kira Egba.

Rundunar 'yan sandan jihar dai ta ce kawo yanzu gawawwakin mutane 45 ne kawai jami'anta suka gano.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Hyancinth Dagala, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa ana kyautata zaton cewa Fulani makiyaya ne suka kai harin a irin rigingimun da akan samu tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

To amma dan majalisar dokokin jihar, Audu Sule, ya gaya wa BBC cewa bisa bayanan da suka samu daga jama'arsu, maharan sun sa kaya irin na soja wasunsu kuma sun yi kitso, kuma alamunsu ba na 'yan Najeriya ba ne.

Ya ce mai yiwuwa wasu ne suka fake da rigingimun yankin suka aikata ta'asa.

Shi ma sakataren kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a jihar ta Benue, Haruna Garba Gololo, ya musanta hannun makiyaya a kashe-kashen na yankin Agatu.

Karin bayani