Zanga zangar adawa da shugabar Brazil

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff

Zanga zangar ta gudana a jihohi goma sha takwas a fadin kasar da kuma Brasilia babban birnin kasar.

Gangami mafi girma ya gudana ne a birnin Sao Paulo inda mutane kimanin dubu dari biyar suka hallara.

Masu zanga zangar na cewa shugabar kasar ta san da lamarin tun da ita ce shugabar kamfanin a lokacin da aka aikata badakalar cin hancin.

Binciken da ofishin babban lauyan gwamnati ya gudanar ya tsame Ms Rousseff daga dukkan wani laifi akan lamarin.