Boko Haram: Har yanzu ba a kwato Damasak ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Najeriya a Maiduguri

A Najeriya rahotanni na cewa sojoji sun fara fafatawa da 'yan kungiyar Boko Haram domin kwato garin Damasak dake jihar Borno daga hannun kungiyar.

Wata majiya daga rundunar sojin Najeriyar ce ta tabbatar da hakan, sabanin rahotannin da aka yi ta baza wa cikin makon jiya, cewa dakarun gwamnati sun kwato garin na Damasak.

Kazalika, wasu majiyoyin soji a Nijar ma sun tabbatar da cewa har yanzu garin Damasak yana karkashin ikon mayakan kungiyar ta Boko Haram.

A ranar 15 ga watan Nuwamban bara ne mayakan kungiyar Boko Haram suka mamaye garin Damasak dake karamar hukumar Mobbar, inda suka kashe mutane 50.

Garin Damasak yana daya daga cikin muhimman garuruwan dake kan iyakar Borno, inda ake noma wake da barkono da tumatir da ake kai wa kasuwannin da dama.