An kashe kusan mutane 50 a Benue

Rahotanni daga jihar Benue a Najeriya sun ce kusan mutane 50 sun rasa rayukansu a wani harin da 'yan bindiga suka kai a jihar.

An kai harin ne ranar Lahadi da safe a kauyen Egba da ke karamar hukumar Agatu.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar, masu yawan gaske, sun yi ta harbin munate ba kakkautawa, sun kuma kona gidajen jama'ar kauyen.

Dan majalisar dokokin jihar ta Benue mai wakiltar yankin, Audu Sule, ya ce da misalin karfe shida na asubahin Lahadi ne maharan suka shiga kauyen.

Jihar Benue dai ta sha fama da rigingmu masu nasaba da kabilanci da kuma tsakanin Fulani makiyaya da manoma inda akan samu hasarar rayuka.

Amma a wannan karon, maharan sun yi kashe-kashen ne ba tare da ware bangaren kabila ko addini ko kuma sana'a ba -- abin da ya kara daure wa jama'ar yankin kai, inji Audu Sule.

Kawo wa yanzu dai hukumomin tsaro a jihar ba su yi wani bayani kan harin ba, amma rahotanni sun ce an tura jami'an tsaro zuwa yankin.

Sai dai akwai korafin cewa sun yi karanci saboda zullumin da ya karu a yankin.

Karin bayani