China ce kasa ta 3 wajen samar da makamai

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption China ta yi wa Jamus da Faransa fintinkau wajen samar da makamai.

Wata cibiya mai bincike a kan zaman lafiya a Stockholm ta fitar da wani rahoto da ke cewa China ce kasa ta uku wajen samar da makamai a duniya, baya ga Amurka da Rasha.

Kafin fitar da wannan rahoto dai, kasashen Jamus da Faransa ne na uku da na hudu a cikin kasashen da ke gaba wajen samar da makamai a duniya.

Yawan cinikin makamai na biliyoyin daloli da kasar ta yi ya haura da kashi 16 cikin 100 a tsakanin shekarar 2010 da 2014, a cewar rahoton da cibiyar ke fitarwa na shekara-shekara.

Adadin ya ninka inda yake cewa Amurka ce a kan gaba da kasha 31 wajen samar da makamai ga kasashen duniya, yayin da Rasha ke biye mata da kashi 27.

Sun bar ragowar kasashe ukun da ke samar da makaman a baya sosai da kashi biyar ga kowacce.

Pakistan da Bangladesh da Myanmar ne kasashen da suka fi yi wa China cinikin makaman. Akwai kuma kasashen Afrika 18 da su ma suke sayen makaman daga China.