An gano tarin makamai a Gamboru

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu makaman 'yan Boko Haram da aka kwato a watannin baya

Dakarun tsaro a Kamaru sun ce sun gano wasu tarin makamai da ake kyautata zaton cewa na kungiyar Boko Haram ne.

Wadannan makamai dai an gano su ne a wani gida bayan sintiri da binciken da dakarun suka gudanar a Gamboru mai makwabtaka da Fotokol a Jamhuriyar Kamaru.

Bayanai sun ce hukumomin Kamaru sun kwashe makaman zuwa birnin Maroua domin ajiya.

Hakan na zuwa ne bayan da dakarun hadin gwiwa na kasashe hudu ke yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeria.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000.