Za mu yi zabe cikin adalci — Jega

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Furofesa Attahiru Jega

Shugaban hukumar zaben Nigeria, Attahiru Jega ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki cikin kasa da makonni biyu masu zuwa.

Jega wanda ya amsa tambayoyi game da zaben a Abuja, ya ce za su yi "iyaka kokarinsu domin tabbatar an yi zabe cikin gaskiya da adalci a ranar 28 ga watan Maris."

"Masu zabe sun karbi katunan dindindin fiye da miliyan 56 daga cikin mutane miliyan 67.8 da suka yi rijista," in ji Furofesa Jega.

Ya kara da cewa "har yanzu akwai katunan zabe na dindindin guda 700,000 da ba a buga ba."

"Ana ta yin rade radin cire ni. Hakan bai dame ni ba. Aikina kawai nake yi," Jega ya jaddada.