Shin kudi yana sa mutum rashin tausayi?

Image caption Da yawan masu kudi basu son taimakon marasa karfi.

"Kudi na gwamna masu gida rana!" Idan aka duba tasirin kudi a kan jama'a, za a ga cewa ya kansa mutum ya zama matsolo, wasu su kan zama masu bishasha da arzikin da suke da shi yayin da wasu kuwa kudin ke rudarsu har su zama marasa tausayi.

Amma me kudi ke sanya mafi yawan mutane a wannan zamani?

A wani bincike da wani masanin halayyar zamantakewar dan adam, Farfesa Paul Piff, ya gudanar, ya yi dubi a kan wai shin wanene ake ganin zai fi tausayin mutumin da yake tafiya a kafa? Shin mai kudi ko talaka?

A tsarin da doka ta tanada dai, dole duk masu tuka mota su tsaya wa duk wani mai son tsallaka titi.

Binciken nasa da ya gudanar a Amurka ya gano cewa, "Da wuya kwarai ka ga masu kananan motoci sun karya wannan doka, amma kusan kashi 50 na masu tuka motoci masu tsada su ne aka fi samu da saba doka."

Shin ya ya tausayinka ya ke?

Bayan ya shafe kimanin tsawon shekaru 10 yana bincike a kan wannan lamari, Farfesa Piff ya kamala binciken nasa mai cike da rudani da cewa a wasu lokutan arziki na sanya mutane da yawa su canza dabi'unsu, inda maimakon su zamo masu tausayi da taimako, sai a ga sun zama masu dagawa.

"Hakika kudi su kan sa mutum ya cimma dukkan burinsa na rayuwa tare da gamsar da bukatunsa," in ji Piff.

"Har ila yau kudi kan dora wa mutum girman kai ya dinga jin ya fi kowa tare da kin mai da hankali kan mutanen da ke kewaye da shi."

Piff ya kara gudanar da wani bincike a dakin gwaje-gwajensa wanda ya nuna cewa ga alama mutane masu dimbin arziki sun fi zalunci da handama da baba-kere kuma su ne basu cika mayar da hankali wajen taimakon wasu ba.

Image caption Binciken masana ya nuna cewa marasa karfi sun fi yin kyauta komai kankantarta.

Masana tattalin arziki masu la'akari da yanayin rayuwa na cewa kamata ya yi hannun talaka ya kasance a dunkule domin amfanin kansa, shi kuwa mai arziki hannunsa ya kasance a bude domin ya taimakawa mutane.

"Mun samu akasin haka. Mutane masu arziki su ne basu cika kyautaba. Da kyar suke iya kyautar wani dan bincine daga cikin dukiyarsu."

"Mutane marasa karfi sun fi kyautatawa, suna iya bayar da kashi 150% na abin da suke da shi fiye da yadda masu kudi ke yi," in ji Farfesa Piff.

Farfesa Piff ya kammala da cewa idan muka samu daula, ba kasafai mu ke dogaro da kowa ba. A zahirin gaskiya ma, idan mutane basu da wadata su kan dogara a kan 'yan uwa da abokan arziki. A don haka mutane kan dauki zumunci da muhimmancin gaske.

Masu kudi kuwa, su kan iya nema wa kansu kwanciyar hankali da zaman lafiya da kuma hanyar warware mafi yawan matsalolinsu. Babu wani abu mai dadi da ya wuce ka ji aljihunka a cike wanda hakan zai iya kawar maka da duk wata damuwa ta kunci. To amma kuma hakan kan hana masu hali sanin yadda rayuwar wasu take.

A tun lokacin da Piff ya wallafa bangaren farko a bincikensa a shekara ta 2010, masana kimiyya da yawa a duniya sun yi kokarin bin sahunsa wajen yin makamancin binciken.

Wasunsu suna samun sakamakon bincikensu ya yi dai dai da na Piff, ya yin da wasunsu kuwa suka sami sakamako akasin nasa.

Kamar dai yadda wani bincike da aka gudanar a kasar Nethalands wanda aka yi amfani da masu dimbin arziki, binciken ya gano cewa masu kudin sun fi talakawa jin kai a duk sanda aka basu kudi komai kankantarsa su ajiye ko su rabar da shi.